A gaskiya bani da wata hujjar yin fashin motoci daga wajen direbobi - Barawon mota

Allah ta'ala ya tona asirin wani matashi mai suna Adesola Yusuf wanda ke fashi da makami ta hanyar karbe motocin yan taxi bayan ya nuna masu karamar bindigar hannu watau Pistol.

Wannan ya biyo bayan wani namijin aiki ne da sashen SARS na rundunar yansandan jihar Lagos suka yi wajen kama Yusuf, ya shaida wa yansanda cewa " Na je Lasu ne a birnin Lagos sai na bukaci a bani shattan mota taxi wanda zai kai ni Egbeda, yayin da muka ci rabin tafiyar, sai na ce direban ya tsaya kuma na fito da karamar bindiga kirar Pistol na nuna masa. Daga bisani na tuka motar kai tsaye na tafi Ibadan".

" A bisa gaskiya na yi nadama wannan aiki, domin bani da wata hujja ko dalilin kwace wannan mota".

Majiyar isyaku.com ta ce Adesola Yusuf, ya kammala karatunsa na babban diploma a harkar kasuwanci, amma ya fada wannan mumunar tabi'a.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN