Zaben gwamnoni: Tinubu ya dakatar da gwamnan APC daga halartar kamfen a jihar sa


Legit Hausa  

Abiola Ajimobi, gwamnan jihr Oyo, ba zai cigaba da halartar yakin neman zaben dan takarar gwamnan a karkashin inuwar jam’iyyar APC a jihar sa ba, kamar yadda majiyar mu ta bayyana ma na.


Ajimobi ya sha kaye a hannun jam’iyyar PDP a zaben kujerar sanatan jihar Oyo ta kudu da ya yi. Gwamnan ya samu kuri’u 92,579 yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Dakta Kola Balogun, ya samu kuri’u 105,720. Wani lamari da ya kara bayar da mamaki shine yadda jam’iyyar PDP ta lashe zaben kujeru 4 daga cikin 5 na ‘yan majalisar wakilai da yankin na jihar Oyo ta kudu ke da su.

Faruwar hakan ne ta saka jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, ya karbi ragamar yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar ta Oyo a jam’iyyar APC domin ganin PDP ba ta kwace jihar ba.

Majiyar mu ta sanar da mu cewar yanzun haka Tinubu ya saye takarar tsohon gwamnan jihar, Alao Akala, domin kara wad an takarar APC, Bayo Adelabu, karfi sannan ya umarci gwamna Ajiomobi ya nesanta kan sa daga wurin yakin neman dan takarar.

Wata majiyar jam’iyyar APC ta shaida wa majiyar mu cewar, “Tinubu ya fahimci cewar jama’ar jihar Oyo na jin haushin gwamna Ajimobi ne ba jam’iyyar APC ba. “Abin tsoron shine zuwan Ajimobi wurin kamfen din Adelabu zai kara lalata damar da APC ke da shin a yin nasara a zaben gwamnoni da za a yi karshen mako.”

 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN