• Labaran yau

  Wasu matasa sun kwace barawo a hannun yansanda suka kashe shi a gaban caji ofis

  Wani barawo ya gamu da mumunar ajali a hannun wasu fusatattun matasa bayan sun kwace shi daga hannun yansanda suka kashe shi kuma suka kone shi a gaban caji ofis na yansandan a garin Ugep na jihar Cross Rivers da tsakar ranar yau.

  Isyaku.com ya gano cewa barawon da aka kone ya kwace babur ne a hannun wani dan acaba bayan ya yi fada da shi, shi kuma dan acaba ya dage suka yi ta dambe domin ya ki ya ba barawon babur.

  Daga bisani ne barawon ya zazzage man fetur da ya riko a wani dan karamin galon a jikin dan acaba kuma ya kunna masa wuta, sakamakon haka dan acaba ya kone shi kuma barawo ya tsere da babur.

  Amma wasu bayin Allah sun tsinci dan acaba a gefen hanya ya kone, sai suka kai shi Asibiti kuma aka shaida wa yansanda, daga bisani kuma sun shiga bincike da ya kai ga kama barawon kuma suka kulle shi a caji ofis.

  Saidai can acaba ya mutu washe gari, lamari da ya sa samari suka harzuka suka je caji ofis suka shiga da karfi suka kwace barawon suka fito da shi suka kashe shi kuma suka banka ma gawarsa wuta a gaban caji ofis na yansanda. 

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wasu matasa sun kwace barawo a hannun yansanda suka kashe shi a gaban caji ofis Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });