Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ke kasancewa


Legit Hausa

A yayin da a ranar Asabar aka gudanar da zaben gwamnoni da kuma kujerar 'yan majalisun dokoki na jiha, mun samu cewa tuni sakamakon zaben wasu rumfunan zabe cikin jihohin musamman na Arewacin Najeriya ya fara bayyana.

Rahotanni sun bayyana cewa, ba ya ga yunkurin aiwatar da magudin zabe yayin da aka cafke wata Mota makire da dangwalallun kuri'u a mazabar unguwar Magwan, an gudanar da zabe lami lafiya yayin da kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Muhammad Wakil, ya tsaya tsayin daka. Kafofin watsa labarai da dama sun ruwaito cewa, ana ci gaba da gwabzawa tsakanin dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APC, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma dan takara na jam'iyyar adawa ta PDP, Abba Kabir Yusuf.

Gabanin tabbatar da rinjayen nasara tsakanin Gwamna Ganduje da Abba Gida-Gida daga bangaren hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ga yadda tiryan-tiryan sakamakon ya kasance a kananan hukumomi 43 cikin 44 na jihar Kano.

NASARAWA LGA APC - 54,349 PDP - 34,297 BEBEJI LGA APC – 17,418 PDP – 18, 533 MADOBI LGA APC – 24,491 PDP – 24, 309 MAKODA LGA APC – 22,788 PDP – 9,253 KUNCHI LGA APC – 16,157 PDP – 13,171 KARAYE LGA APC – 18,770 PDP – 17, 163 KIBIYA LGA APC – 15,760 PDP- 17373 ALBASU LGA APC- 25,358 PDP – 18,401 GARKO LGA APC – 16,952 PDP – 12,295 BUNKURE LGA APC – 20,407 PDP – 20,222 RANO LGA APC – 16,694 PDP – 14,892 DANBATTA LGA APC – 24,686 PDP – 18,696 BAGWAI LGA APC- 20,768 PDP- 18,511 TSANYAWA LGA APC -21,972 PDP -11,501 TOFA LGA APC – 17,506 PDP – 13,885 GWARZO LGA APC – 27,015 PDP – 24,773 GABASAWA LGA APC – 18,215 PDP – 14,679 SHANONO LGA APC – 20,691 PDP – 14,503 KABO LGA APC – 27,522 PDP – 16,233 SUMAILA LGA APC – 23,934 PDP – 16,606 AJINGI LGA APC – 17,711 PDP – 14,585 GEZAWA LGA APC – 20,642 PDP – 24,151 BICHI LGA APC – 31,958 PDP – 27,644 WARAWA LGA APC – 14,599 PDP – 15,114 KIRU LGA APC – 28,765 PDP – 27,868 RIMINGADO LGA APC – 19,453 PDP – 13,777 GWALE LGA APC – 23,871 PDP – 41,591 WUDIL LGA APC – 18,589 PDP – 18,220 TUDUN WADA LGA APC – 27,917 PDP – 21,556 DOGUWA LGA APC – 20,696 PDP – 12,642 DAWAKIN KUDU LGA APC – 25,657 PDP – 30,901 MINJIBIR LGA APC – 17,707 PDP – 17,952 GARUN MALAM LGA APC – 14,765 PDP – 14,446 TARAUNI LGA APC – 21,734 PDP – 35,314 GAYA LGA APC- 19,202 PDP – 18,090 ROGO LGA APC – 23,859 PDP – 27,342 UNGOGO LGA APC – 26,843 PDP – 42,247 DAWAKIN TOFA LGA APC- 32,945 PDP- 17,418 KURA LGA APC – 22,390 PDP – 24,410 KUMBOTSO LGA APC- 24,751 PDP 40-417 KANO MUNICIPAL APC – 32,394 PDP – 57,781 TAKAI LGA APC – 19,070 PDP – 14,119 DALA LGA APC – 32,530 PDP – 60,082 FAGGE LGA APC – 18,370 PDP – 27,344

A halin yanzu Gwamna Abdullahi Ganduje ya samu gamayyar kuri'u 987,819, yayin da abokin adawar sa na jam'iyyar PDP, Abba Gida-Gida ya lashe kuri'u 1,014,474. Sai dai hukumar INEC ta kaddamar da cewa sai an sake gudanar da zaben a wasu wurare cikin jihar Kano.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN