• Labaran yau

  Tsabar kishi: Amsa gaisuwar miji ya sa mata ta kwara wa makwabciya tafasashshen ruwan zafi

  Yansanda a birnin Lagos sun cafke wata mata mai suna Mrs Josephine bayan ta watsa ma wata mata makwabciyarta mai suna Mrs Blessing Christopher tafasashshen ruwan zafi a jikinta saboda ta amsa gaisuwan mijinta.

  Blessing ta ce " Ina cikin dakin dafa abinci ina girki, sai maigidan Josephine ya wuce kuma ya gaishe ni ni kuma na ce mashi barka da zuwa yallabai, domin muna zaune a gida daya amma kowa da nashi bangare.

  Daga nan ne fa Josephine ta fito ta gargade ni cewa idan na sake gaida mijinta ko na sake amsa gaisuwarsa zan ga abin da zai faru, amma sai na ce mata amsa gaisuwa ya zama laifi ne kenan ? sai ta ce da ni in jira in gan abin da zai faru.

  Ni dai na ci gaba da girki na, sai bayan wani likaci Josephine ta zo da tukunya cike da ruwan zafi, amma maigidanta ya yi kokarin hanata domin ya yi sauri ya shiga gabana domin ya hanata zuba mini ruwan zafin, amma sai ta zagayo ta bayana ta watsa mani ruwan zafin wanda ya yi sanadin yi mani rauni ta hanyar kone fatar jikina".

  Yanzu haka dai yansanda suna bincike a akan lamarin.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Tsabar kishi: Amsa gaisuwar miji ya sa mata ta kwara wa makwabciya tafasashshen ruwan zafi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });