Kasashen Afirka ta Yamma za su fara amfani da samfurin kudi na bai daya a 2020 - ECOWAS


Legit Hausa

Kungiyar tattalin arzikin kasashen yankin Afirka ta Yamma, ECOWAS (Economic Council of West African States), ta ce za a fara amfani da samfurin kudi na bai daya cikin wasu zababbun kasashe da yankin ya kunsa a shekarar 2020.

Shugaban majalisar tarayyar kasar Senegal, Moustapha Niasse, shi ne ya bayyana hakan yayin jagorantar wani taron karawa juna sani a jiya Litinin tare da shugaban kungiyar ECOWAS, Jean-Claude Kisse Brou da kuma kakakin kungiyar, Moustapha Cisse Lou.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, an gudanar da wannan taro domin tattauna batutuwa na kalubalen kaddamar da amfani da samfurin kudi na bai daya cikin kasashen yankin Afirka ta Yamma.

Kakakin kungiyar, Moustapha Cisse Lou ya bayyana cewa, amfani da samfurin kudi na bai daya cikin kasashen ECOWAS zai yaye shinge da kuma shamaki na harkokin kasuwaci da mu'amala ta kudade domin habaka tattalin arziki.

Ya yi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da su jajirce tare da tsayuwar daka wajen tabbatuwar wannan muhimmin lamari na amfani da samfurin kudi na bai daya a kasashen ECOWAS domin kyautatuwar fidda A'i daga Rogo.

Majalisar Shugabannin kungiyar ECOWAS ta kuma yi kira ga gwamnatocin kasashen yankin kan tumke damarar su tare da cimma matsaya ta karbar wannan kudiri hannu biyu-biyu gabanin shekarar 2020 da aka kayyade domin kaddamar da samfurin kudi na bai daya a kasashen yankin.

 DAGA ISYAKU.COM

 Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

 Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN