Buhari ya fadi irin kalar mutanen da zai bawa mukami a zango na biyu


Legit Hausa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce mutane ma su kima da kishin Najeriay ne kawai za su mukamai a nade-naden da zai yi a sabuwar gwamnatin sa.

Kazalika ya yi alkawarin kara yawan mata da matasa a cikin sabbin nade-naden saboda irin muhimmiyar gudunmawar da su ka bayar wajen samun nasarar sa a zaben da aka yi a karshen makon jiya. Ya bayyana cewar gwamnatin sa ba zata bawa mata da matasa kunya ba.

Buhari ya yi wadannan kalamai ne yayin gabatar da jawabi a wurin liyafar da mata da matasan jam’iyyar APC su ka shirya ma sa omin taya shi murnar samun nasarar lashe zaben kujerar shugaban kasa a karo na biyu. Ya ce samar da taki a kan farashi mai rahusa ya kawo habakar samun amfanin gona da kuma rage yawan shigowa da kayan abinci daga kasashen ketare.

Buhari ya yi kira ga matasan Najeriya da su rungumi noma domin kawar da yunwa da samun hanyoyin dogaro da kai. Kazalika, ya soki shekaru 16 na mulkin PDP tare da zargin su da barnatar da dumbin dukiyar kasa da Najeriya ta samu a lokacin.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN