APC ta ci zaben gwamna a Jigawa da Kebbi, ba a kammala na Sokoto ba


Legit Hausa

Sakamako na karshe da hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta bayyana a Kebbi, ya nuna cewar gwamnan jihar, Abubakar Atiku Bagudu na jam’iyyar Kebbi ya sake lashe zaben gwamnan jihar a karo na biyu.

Bagudu na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 673,717, adadin da ya bashi nasara a kan babban hamayyar sa na jam’iyyar PDP, Sanata Isah Galaudu, wanda ya samu kuri’u 106,633, sai kuma Malam Ka’oje na jam’iyyar SDP da ya samu kuri’u 7,444. Sakamakon zaben kujerar gwamna da hukumar zabe ta sanar a Jihar Jigawa ya tabbatar da cewar gwamnan jihar mai ci, Mohammed Abubakar Badaru, ya sake lashe zaben kujerar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Badaru ya samu kuri’u 810,933 da su ka bashi nasara a kan babban abokin hamayyar sa, dan takarar jam’iyyar PDP, Malam Aminu Ibrahim Ringim, wanda ya samu adadin kuri’u 288,356, sannan sai dan takarar jam’iyyar SDP, Bashir Adamu, wanda ya zo na uku da adadin kuri’u 32,894 Malam Aminu Ringim ne dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP da gwamna Badaru ya fara kayar wa a zaben shekarar 2015 lokacin da jihar Jigawa ke hannun jam’iyyar PDP.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta (INEC) ta bayyana zaben kujerar gwamna da aka yi ranar Asabar da ta gabata a jihar Sokoto a matsayin wanda bai kammalu ba. Baturiyar zabe a jihar, Farfesa Fatima B. Mukhtar, ce ta bayyana da duku-dukun safiyar yau, Litinin, bisa hujjar cewar adadin kuri’un da aka soke ya fi adadin banbancin kuri’un da ke tsakanin ‘yan takarar biyu.

Kamar yadda sakamakon zaben na karshe ya nuna, jam’iyyar PDP ta samu nasara da adadin kuri’u 489,558 yayin da jam’iyyar APC ke biye ma ta da adadin kuri’u 486,145. Ana fafata wa a matakin kujerar gwamna a jihar Sokoto tsakanin gwamna mai ci, Aminu Waziri Tambuwal na jam’iyyar PDP, da babban abokin hamayyar sa, Ahmad Aliyu na jam’iyyar APC. 75,403 ne adadin kuri’un da aka soke daga mazabu 136 da ke fadin kananan hukumomin jihar Sokoto 22, kamar yadda baturiyar zaben ta sanar.

 DAGA ISYAKU.COM

 Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN