An kashe mutum daya sakamakon wani hargitsi da tashin hankali a Kakuri a karamar hukumar Kaduna ta kudu a jihar Kaduna.
Rahotanni sun ce tashin hankalin ya faru ne tsakanin magoya bayan jam'iyun APC da na SDP a lokacin yawon yakin neman zabe a Kakuri ranar Laraba 6 ga watan Maris, 2019.
Hakazalika majiyarmu ta ce rikicin ya sa matasa sun yi amfani da mugan makamai kamar wukake kuma suka ta yi ma junansu raunuka lamari da ake zargin ya kai ga mutuwar wani matshi mai suna Daniel Adamu.
Bayanai sun ce an barnata dukiyoyin jama'a, shaguna, motoci tare da yin sace--sacen ababe da dama.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi