Al'umman Borgu mazauna jihohin Kebbi,Niger da Kwara sun kai ziyara ga shugaba Muhammadu Buhari karkashin jagorancin Mai martaba Sarkin Borgu Alhaji Muhammed Haliru Dantoro a fadar shugaban kasa ranar Alhamis.
Tawagar ta kunshi wasu manyan yan siyasa har da Sanata Aliyu Abdullahi na jam'iyar APC, tare da Sarakunan Borgu, Kaima, Ilesha Gwanara, Yanshikira da kuma Okuta.
Majiyar isyaku.com ta jiyo basaraken yana cewa "Al'umman Borgu mazauna jihohin Kwara,Niger da Kebbi hade kansu yake wajen neman ganin an kirkiro masu jiharsu ta Borgu".
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi