Type Here to Get Search Results !

Zaben 2019: Sakamakon zabe ya fara bayyana daga Jihar Kaduna


Legit Hausa

Mun ji labari cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya doke Atiku Abubakar a cikin karamar hukumar Giwa da ke cikin jihar Kaduna. Jam'iyyar adawa ta samu kuri'a 9838 ne inda APC kuma ta ci 45, 574. Sakamakon da ya fito daga karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna ya nuna cewa Atiku Abubakar ya samu nasara a zaben jiya.

Jam'iyyar PDP ta samu kuri'a 33, 647 ne inda ta lallasa jam'iyyar APC mai kuri'a 6, 907 inji hukumar INEC. Yanzu nan mu ke jin labari cewa ana shirin fara kirga kuri’un Sanatoci na Yankin Kaduna inda Sanata mai ci Kwamared Shehu Sani na PRP ya kara da Uba Sani wanda ya fito a jam'iyyar APC mai mulki da kuma Lawal Abubakar na PDP.

A baya dai kun ji cewa Bala Bentex na jam'iyyar APC ya rasa akwatin kauyen sa a hannun 'dan takarar PDP wanda ke kan mulki watau Sanata Danjuma Laah. Haka kuma Sanata mai-ci Sulaiman Hunkuyi zai kara da Sulaiman A.

Kwari. Zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa yana cigaba da zuwa mana daga Kaduna. Dazu nan mu ka ji cewa Mataimakin Gwamnan Kaduna mai neman takarar Sanata a Kudancin jihar ya gaza kawowa Jam'iyyar APC kuri'ar sa.

Barnabas Bala Bantex ya samu kuri’a 2113 ne, yayin da shi kuma ‘dan takarar PDP wanda shi ne yake kan mulki ya samu kuri’u 2, 301 a Garin Manchok. Haka kuma shugaba Buhari ya samu kuri'a 1443 ne inda Atiku ya samu kuri'u 2991.

A wani akwati da ke cikin Unguwar Dan Masani a yankin Rigachikun, mun ji cewa shugaba Muhammadu Buhari ya samu kuri'a 1150 inda Atiku Abubakar ya samu kuri'u 5. Sakamakon zaben dai su na cigaba da nuna nasarar APC.

Sakamakon zabe yana kara shigo mana daga jihar Kaduna inda mu ka ji cewa PDP tayi nasara a akwati mai lamba na 019 da na 020 a cikin karamar hukumar Sabon Gari a Zaria. Buhari ya samu kuri'a 91 ne inda Atiku kuma ya samu kuri'u 122. A yankin Kwarbai a cikin garin Zariya, APC ta samu kuri'a 1000 cif inda Atiku kuma ya samu kuri'a 49.

Sai dai ba mu da tabbacin wannan sakamako daga bakin INEC. Haka kuma APC ta lallasa PDP a zaben 'Yan majalisu da aka yi a Yankin. A zaben 'yan majalisa kuma da aka yi, APC ta samu kuri'a 83 a kujerar Sanata inda PDP kuma ta samu kuri'u 128. A kujerar majalisar wakilai na tarayya kuma PDP ta samu kuri'a 125. jam'iyyar APC mai mulkin jihar ta samu kuri'a 80 ne a zaben. Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya sha kasa a akwatin da yayi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisan tarayya a Unguwar Sarki a cikin jihar Kaduna. APC ta samu kuri'a 236 yayin da Shehu Sani ya samu kuri'a 51 rak a akwatin na sa.
 

DAGA ISYAKU.COM

 Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN