Type Here to Get Search Results !

Yanzu yanzu: Yan daba sun kama kwamishinan yansanda, sun yi garkuwa da shi

An kara yawan jami'an tsaro a karamar hukumar Twon Brass a jihar Bayelsa bayan wasu yan daban siyasa sun dauke wani mataimakin Kwamishinan yansanda mai suna Kola Okunola wanda shi ne mataimakin Kwamishiinan yansanda na sashen F-SARS a jihar Bayelsa.

Rahotanni sun ce wasu matasa magoya bayan jam'iyar APC ne suka wulakanta wannan kwamishina bisa zargin yana kokarin hada baki da 'yan jam'iyar PDP domin a canja sakamakon zabe na karamar hukumar.

Saidai jam'iyar PDP a karamar hukumar ta ce wadanda suka ci zarafin babban jami'in dansandan a bainar jama'a yan daba ne masu goyon bayan tsohon gwamnan jihar Bayelsa Chief Timipre Sylva
 da kuma dan majalisa mai wakiltar Brass 1 a majalisar dokokin jihar Bayelsa Israel Sunny-Goli..

Sakataren gwamnatin jihar Bayelsa Mr. Kemela Okara ya yi zargin cewa wani da ake kira Sunny Goli ne ya jagoranci yan daban kuma suke matsa wa kwamishinan yansandan lamba tare da soji domin ya aminta da sakamakon da ba haka yake ba a karamar hukumar.

Ya kuma yi zargin cewa bayan matsin lamba amma babban jami'in yansandan ya ki amincewa, sai cacar baki ya shiga tsakanin wani jai'in soji mai mukamin Manjo da mataimakin kwamishinan yansandan, daga bisani kuma sai yan daban suka dauke DCP na yansandan suka ja shi wulakance suka shiga ruwa da shi kuma suka tube shi zindir a wani tsibiri.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN