Yan bindiga sun halaka soji suka yi wa jama'a kisan gilla a jihar Katsina

Wasu yan bindiga sun kashe wani jami'in soji da wasu kauyawa a kauyen Kasai wanda ke kilomita 10 daga garin Batsari na karamar hukumar Batsari a jihar Katsina ranar Lahadi.

Rahomtanni sun ce lamarin ya faru da misalin karfe 10 na safe, kuma ya yi sanadin sace shanaye akalla 200.

Wata majiya ta ce yan bndigan su da yawa sun shigo kauyen kuma suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi bayan yan kauyen sun fuskance su.

Kakakin hukumar yansanda na jihar Katsina Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya kara da cewa yan bindigan sun shigo ne daga gandun Rugu kuma suka yi ma jami'an soji kwanton bauna suka halaka daya. Amma ya musanta cewa an sace shanu 200 a harin.
 .
DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN