• Labaran yau

  Ya Kashe Masoyiyarsa Uwar Yara 5 Ya Bizineta A Gidansa Bayan Ya Damfareta N530.000

  Rundunar 'yansandan jihar Ogun ta cafke wani mutum mai suna Kazeem Adebayo bisa zargin kashe masoyiyarsa mai suna Abosade Adesanya wacce mahaifiyar yara biyarce.

  Kakakin hukumar 'yansandan jihar Ogun ya shaida wa manema labari haka ranar Juma'a. DSP Abimbola Oyeyemi ta ce Kazeem ya kira masoyiyarsa Abosade a wayar salula ranar 25 ga watan Janairu, ya shaida mata cewa ta zo da kudi N530.000 domin zai sayar mata da wani Fili.

  Amma kafin Abosade ta bar gida, sai ta shaida wa mahaifiyarta cewa za ta tafi gidan Kazeem, kuma tun wannan ranar Abosade bata dawo gida ba. Wannan lamari ya sa mahaifiyarta ta kai kara wajen 'yansanda kuma bayan sun gudanar da bincike sai suka bankado yadda Kazeem ya kashe masoyiyarsa Abosade  da wani kulki, daga bisani ya bizine ta a cikin gidansa ya dauke kudin da ta kawo masa N530.000.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ya Kashe Masoyiyarsa Uwar Yara 5 Ya Bizineta A Gidansa Bayan Ya Damfareta N530.000 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });