Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa za ta bi Umarnin Shugaba Muhammadu Buhari, matsawar ya bada odar cewa duk wanda ya fizgi akwatin zabe, to a bindige shi kawai, jaridar Premium Times ta ruwaito.
Hukumar sojin sun yi wannan karin haske ne biyo bayan
kakkausan furucin da Buhari ya yi a ranar Litinin, 18 ga watan Fabrairu cewa
duk wanda ya saci akwatin zabe, to ya yi a ta bakin ran sa. Wannan kalami na
Shugaban kasar a janyo ce-ce-ku-ce , suka da kuma caccaka, duk da dai magoya
bayan shugaban na ta kokarin kare dalilan sa na yin furucin.
Dokar zabe dai ta tanadi daurin shekaru biyu ga duk wanda
aka kama ya saci akwatin da aka jefa wa kuri’a. Shi kuma Buhari ya ce a harbe
wanda ya saci akwati ya tsere kawai. Ya yi wannan kakkausan kalami ne a taron masu
ruwa da tsaki na jam’iyyar APC jiya Litinin a Abuja.
A na su bangaren, sojojin Najeriya sun kara wa wannan
tankiya zafi, yayin da Kakakin su Sagir Musa ya bayyana wa majiyarmu ta Premium
imes cewa idan dai shugaban kasa wanda kuma shi ne Babban Kwamandan sojin
Najeriya gaba daya, ya bayar da umarni ga sojoji, to babu tantama, ba tababa,
kuma babu wani bata lokaci, aiwatarwa kawai za su yi.
A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto cewa d an
takaran kujeran shugaban kasa a jam’iyyar Peoplea Democratic Party (PDP), Atiku
Abubakar, a jiya Litinin, 18 ga watan Fabrairu yace shugaban kasa Muhammadu
Buhari ya nuna “kalan shi tare da rashin girmama kundin tsari mulki”, ta hanyar
furta cewa a bakin ran duk wanda yayi yunkurin sace akwatin zabe.
Atiku, a wani jawabin da yayi ta hannun kakinsa, Phrank
Shaibu, yace barazana da mutuwa ga mutane a halin shirin gudanar da zabe “kalma
ce dake hadda sa rikicin zabe”. Atiku wanda ya nuna rashin amincewarsa akan
shirin tura sojoji a zaben 2019, inda yake bayyana hakan a matsayin rashin
dacewa ga damokardiyya, yayi Allah wadai da dabarun tsoratarwa da Gwamnatin
Tarayya ke shiryawa.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi