• Labaran yau

  Kotu Ta Garkame Saurayi A Kurkuku Bayan Ya Kashe Matashi Domin Ya Ki Ya Karbi Musulunci

  Wata Kotun Majistare a Ebute Meta da ke birnin Lagos ta tasa keyar wani saurayi mai suna Habeeb Eletu dan shekra 26 zuwa Kurkuku bisa zargin kashe wani matashi ta hanyar daba masa wuka a kirji domin ya ki ya karbi addinin Musulunci.

  Mai gabatar da kara Safeto Kehnde Omisakin, ta shaida wa Kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne ranar 22 ga watan Janairu da karfe 9 na dare a garin Awoyaya da ke Ibeju-Lekki a birnin Lagos.

  Ta shaida wa Kotu cewa wanda ake tuhuma ya fito a fusace cikin wannan dare kuma ya dinga fuskantar duk wanda ya hadu da shi cewa ya karbi shahadar Musulunci, idan mutum ya ki kuwa sai ya yi barazanar cewa zai kashe shi domin jininshi ya halalta.

  Safeto Kehinde ta kara da cewa garin haka ne Habeeb ya kashe wannan matashi mai suna Ojo bayan ya daba masa wuka a kirji kuma ya dinga barnata dukiyan mutane ta hanyar farfasa duk abinda ya samu matukar wanda ya fuskanta bai karbi Musulunci ba.

  Hakazalika Habeeb ya barnata wata mota kirar Toyota Camry mai lamba LND 568 FM (Lagos) da kuma wata mota kirar Honda saloon mai lamba GGE 478 AM (Lagos).

  Alkalin Kotun Mrs O.A. Komolafe ta tasa keyar Habeeb zuwa Kurkuku har zuwa ranar 8 ga watan Fabrairu 2019 domin ci gaba da shari'a.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotu Ta Garkame Saurayi A Kurkuku Bayan Ya Kashe Matashi Domin Ya Ki Ya Karbi Musulunci Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });