Idan ka shirya satar akwatin zabe, na shirya aika ka lahira - Wata macen soja

Wata sojin Najeriya da ta isa wajen da aka turata aikin bayar da tsaro saboda zabe na ranar Asabar ta sha alwashin cika umarnin shugaban kasa na bindige duk wanda ya sace akwatin zabe.

A wani hoto da ya bayyana a shafin intanet, an ga mace soja rike da bindigarta ta ce " Idan ka shirya sace akwatin zabe ranar Asabar, ni kuma a shirye nake in aika ka lahira ranar Asabar".

Kakakin hukumar soji Sagir Musa ya ce" Tunda shugaban kasa ya bayar da umarni ga rundunar sojin Najeriya, wajibi ne mu aiwatar da umarninsa ba tare da wata-wata ba".

Idan baku manta ba, shugaba Buhari ya ba soji umarnin su bindige duk wanda ya sace akwatin zabe azabuka da za a yi na 2019.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post