Leadershipayau.com
A jiya alhamis ne wasu gungun matasa suka kona wata mata da
ranta a garin Nasarawan Eggon. Abin ya faru ne a tsakiyan gari kusa da ofishin
hukumar tsaro ta farin kaya ta (NSCDC), abin ya faru ne da misalin karfe daya
na rana. Lokacin da wasu kananan yara suka taso daga Makarantar Boko, sai matar
ta kira daya daga cikin kananan yaran ta janye shi gefe.
A lokaci guda hankalin jama’a ya kai kanta, saboda ita matar
tana da siffar Mahaukata, da ka ganta, ka ga mahaukaciya. Duk da cewa jama’a sun
lura babu alamar hauka a tattare da ita, amma shigarta ta mahaukata ne.
Kuma ya zo daidai da halin da al’umman garin Nasarawan
Eggon, suke ciki na fama da sace-sacen yara kanana. Hakan ya sanya suke zargin
ire-iren wadannan mahaukatan saboda duk da cewa ita a siffar mahaukata take,
amma tana amsa wayar salula na hannu.
Kiran yaron da ta yi zuwa wani sako, kan ka ce me! Jama’a
suka yi ca a kanta, duk da cewa shedun gani da ido sun ce a lokacin da aka
kamata da yaron ta fara magana cewa ba ita kadai ba ce, ta fara jawabi amma
zuwan wasu jama’an suka afka mata da duka da sanya wuta nan take ta yi kasa.
Duk da kokarin da jami’an tsaron (NSCDC) suka yi domin su
cece ta a hannun matasan amma abin ya ci tura har sai da suka kona ta.
Ya zuwa lokacin rubuta wannan labarin babu wani jawabin da
Hukumar (NSCDC) ko ta ‘yan sanda suka fitar duk da kokarin mu na neman jin ta
bakin jami’an tsaron, amma ba mu samu lokaci ba, saboda rashin shigar wayansu.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi