Legit Hausa
Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon
kasa, EFCC ta cafke wani babban mai kula da kudaden da ake kashewa a takarar
dan takarar shugaban kasa na jam’yyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, mai suna Uyi
Giwa-Osagie.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wata majiya ta karkashin kasa ta
bayyana cewa EFCC ta kama Uyi ne a ranar Litinin, 18 ga watan Feburairu, amma
ta sakeshi bayan ta gudanar da bincike akansa tare da yi masa wasu yan
tambayoyi na tsaown sa’o’i 9 a ofishinta. Shi dai Uyi babban lauya ne, kuma
shine babban mai kula da duk kudin da ake kashewa a takarar Atiku Abubakar,
wanda ya hada har da yakin neman zabe, don haka yana daya daga cikin amintattu,
na hannun dama kuma na kusa da Atiku.
“Atiku baya kashe kudi a takararsa kai tsaye, Uyi Giwa ne ke
kashe duk kudin da ake bukata a yakin neman zaben Atiku, ta hannunsa Atiku yake
antaya kudi cikin yakin neman zabensa. “Don haka kamashi da EFCC tayi ka iya
haifar da takarar Atiku, musamman game da zirga zirgan wakilan zabe da zasu
kare mana kuri’unmu a kowanne rumfa da kuma biyansu kudadensu.”
Inji wani kusa a kwamitin yakin neman zaben Atiku. Shima
tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonatha, Reno Omokri, wanda a
yanzu yana cikin jiga jigan dake tsara yakin neman zaben Atiku Abubakar ya
bayyana bacin ransa da kamen da EFCC ta yi ma Uyi, inda yace anyi haka ne don
yi ma takarar Atiku zagon kasa.
“Akan me EFCC za ta kama lauyan Atiku Uyi tafe da jami’an
Yansanda guda 25 dauke da muggan makamai? Kodai dama shirin su kama duk wanda
ke tare da Atiku yasa suka dage zaben? Laifi ne ka zama lauyan Atiku? Ya zama
dole EFCC ta bayyana ma yan Najeriya dalilin kama Uyi.” Inji shi.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi