Da dumi dumi: Mutane da dama sun mutu yayin da aka kai ma Kwankwaso hari a jahar Kano


Legit Hausa

Wani rahoton da muka samu da dumi dumi ta ruwaito wasu matasa yan daba sun kai ma tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso hari a daidai kauyen Kofa cikin karamar hukumar Bebeji ta jahar Kano, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an kwashi gawarwakin mutane da dama daga bangaren magoya bayan Kwankwaso wanda aka fi saninsu da suna yan Kwankwasiyya da kuma bangaren yan daban da suka kai masa harin.

Sai dai wasu majiyoyi sun danganta yan daban da suka kai ma Kwankwaso haring a yaran dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru da Bebeji, Abdulmuminu Jibrin, wadanda suka tare ma Kwankwaso hanya.
 

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post