Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya sallami Kwamishinan watsa labarai na jihar Mr Bello Muhammad-Goronyo daga mukaminsa da yammacin Talata, sakamakon ficewar Kwamishinan daga jam'iyar PDP zuwa jam'iyar APC .
Darakta janar kan sadarwa da hulda da jama'a na Gwamna Aminu Tambuwal Mallam Abubakar Shekara, ya shaida wa manema labarai haka, ya ce " Gwamna Aminu Tambuwal ya sallami Barista Bello Goronyo daga mukamin Kwamishinan watsa labarai na jihar Sokoto nan take. Kuma ya umarci Sakataren dindindim na ma'aikatan watsa labarai na jihar Sokoto ya rike ma'aikatar".
Ya kara da cewa an sallami Kwamishinan ne bisa zargin yin zagon kasa ga ayyukan alhairi da Gwamnati ta yi.
Shi dai tsohon Kwamishinan ya ayyana ficewarsa ne daga jam'iyar PDP a wani gangamin taro na jam'iyar APC a Goronyo da yammacin Talata.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi