Hukumar tsaron farin
kaya ta DSS, ta gayyaci wani babban jami’i a hukumar zabe mai zaman
kanta, INEC, wanda ya sabbaba dage zaben 2019 da kwanaki bakwai, Mista
Okechukwu Ibeanu, domin amsa tambayoyi bisa wasu tuhume tuhumen da take
masa.
Mista Ibeanu, shine kwamishinan INEC mai kula da tsare tsare da zirga
zirga, sa’annan shine ke wakiltar yankin kudu maso gabashin Najeriya a
hukumar, sai dai ana tuhumarsa da sakaci wajen gudanar da aikinsa, wanda
hakan yasa dole aka dage zaben 2019.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito an jiyo shugaban hukumar INEC, Farfesa
Mahmoud Yakubu yana bayyana bacin ransa game da dage zaben na 2019,
wanda ya danganta hakan ga bita da kullin da wasu keyi ma hukumar, da
kuma rashin isan kayan aiki zuwa inda suka kamata cikin lokaci.
A matsayinsa na kwamishinan tsare tsare da zirga zirga, hakkin tabbatar
da isan kayan aikin zabe zuwa inda suka kamata ya rataya ne a wuyan
Ibeanu, bayan an amshe mukamin daga hannun Amina Zakari a watan Oktoban
shekarar data gabata.
Ana sa ran da misalin karfe 2 na ranar Talata ne Ibeanu zai gurfana
gaban hukumar DSS a babban ofishinta dake babban birnin tarayya Abuja,
sai dai an jiyo Ibeanu yana bayyana ma abokansa cewa ana masa barazana.
Rahotanni sun tabbatar da cewar anyi kutse cikin gidansa dake garin
Enugu, haka zalika an fasa motarsa, inda aka kwashe masa kayayyaki da
dama daga ciki har da kwamfutar tafi da gidanka. Sai dai dama an jiyo
shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin gudanar da binciken INEC
bayan zabe don gano gaskiyar abinda yasa ta dage zaben.
Amma a wani yanayi na waiwaye adon tafiya, an bankado wata kasida da
Farfesa Ibrahim Jibrin ya rubuta a shekarar 2015 lokacin da aka nada
Ibeanu mukamin kwamishinan INEC, inda ya zargeshi da niyyar dabbaka
manufofi da muradin kungiyoyin rajin kafa kasar Biyafara a INEC.
A yanzu dai ana nan ana tafka muhawara akan wannan tsohuwar kasida ta
Farfesa Ibrahim, inda wasu ke danganta tsaikon da aka samu a zaben 2019
ga burin Ibeanu na tabbatar da manufofin yan Biyafara, wanda hakan har
sun fara kiraye kirayen a tsigeshi da taken #INECIbeanuMustGo. Read
more: https://hausa.legit.ng/1222783-babban-jami-hukumar-inec-da-ya-yi-sanadiyyar-zage-zabe-zai-gurfana-gaban-dss.html
Legit Hausa
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS, ta gayyaci wani babban jami’i a hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, wanda ya sabbaba dage zaben 2019 da kwanaki bakwai, Mista Okechukwu Ibeanu, domin amsa tambayoyi bisa wasu tuhume tuhumen da take masa.
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS, ta gayyaci wani babban jami’i a hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, wanda ya sabbaba dage zaben 2019 da kwanaki bakwai, Mista Okechukwu Ibeanu, domin amsa tambayoyi bisa wasu tuhume tuhumen da take masa.
Mista Ibeanu, shine kwamishinan INEC mai kula da tsare tsare
da zirga zirga, sa’annan shine ke wakiltar yankin kudu maso gabashin Najeriya a
hukumar, sai dai ana tuhumarsa da sakaci wajen gudanar da aikinsa, wanda hakan
yasa dole aka dage zaben 2019.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito an jiyo shugaban hukumar INEC,
Farfesa Mahmoud Yakubu yana bayyana bacin ransa game da dage zaben na 2019,
wanda ya danganta hakan ga bita da kullin da wasu keyi ma hukumar, da kuma
rashin isan kayan aiki zuwa inda suka kamata cikin lokaci.
A matsayinsa na kwamishinan tsare tsare da zirga zirga,
hakkin tabbatar da isan kayan aikin zabe zuwa inda suka kamata ya rataya ne a
wuyan Ibeanu, bayan an amshe mukamin daga hannun Amina Zakari a watan Oktoban
shekarar data gabata.
Ana sa ran da misalin karfe 2 na ranar Talata ne Ibeanu zai
gurfana gaban hukumar DSS a babban ofishinta dake babban birnin tarayya Abuja,
sai dai an jiyo Ibeanu yana bayyana ma abokansa cewa ana masa barazana.
Rahotanni sun tabbatar da cewar anyi kutse cikin gidansa dake garin Enugu, haka
zalika an fasa motarsa, inda aka kwashe masa kayayyaki da dama daga ciki har da
kwamfutar tafi da gidanka.
Sai dai dama an jiyo
shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin gudanar da binciken INEC bayan
zabe don gano gaskiyar abinda yasa ta dage zaben. Amma a wani yanayi na waiwaye
adon tafiya, an bankado wata kasida da Farfesa Ibrahim Jibrin ya rubuta a
shekarar 2015 lokacin da aka nada Ibeanu mukamin kwamishinan INEC, inda ya
zargeshi da niyyar dabbaka manufofi da muradin kungiyoyin rajin kafa kasar
Biyafara a INEC.
A yanzu dai ana nan ana tafka muhawara akan wannan tsohuwar
kasida ta Farfesa Ibrahim, inda wasu ke danganta tsaikon da aka samu a zaben
2019 ga burin Ibeanu na tabbatar da manufofin yan Biyafara, wanda hakan har sun
fara kiraye kirayen a tsigeshi da taken.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi