ISYAKU.COM ya tattaro daga Hajiya Maryan cewa kudade da 'yan kungiyar suke bin gwamnatin jihar Kebbi, sun hada da kudaden kwangilar ciyar da daliban jihar Kebbi na watan Nuwamba 2014, Janairu 2015, Fabrairu 2015, Maris 2015, Aprilu 2015, da kuma Mayu 2015.
Alh Chindo ya ce " kungiyar mu tana bin gwamnatin jihar Kebbi bashin fiye da Biliyan daya da kari".
Ya kara da cewa " Duk kokarin da ake yi mun yi, domin dai mun rubuta takarda zuwa ga kowane Sarki mai Sanda a jihar Kebbi, mun aika masa da takarda, kowane Sanata da ke kan gado yanzu, mun aika mashi takarda, Darakta SSS na jihar Kebbi da Kwamishinan 'yansanda mun aika masu da takarda, Kwamishinan Ilimi mun bashi takarda.Gwamnati ta nada kwamiti na musamman ta kuma tabbatar da muna binta wannan bashi, amma daga karshe bamu sami wani gamsashshen bayani ba har tsawon shekara hudu".
"Abin ban mamaki duk wadanda ke wannan wurin kashi 85 duk 'yan APC ne, kuma muna nan a APC har yanzu. A ko da yaushe akan ce mana wasu ma'aikata sun dauke kudin , shin su waye wadannan da suka dauke kudin ?. Mun yi mitin da Gwamna ya shaida mana cewa za a biya kudaden, ammam har yau ba a biya ba, yau kusan shekara hudu".
" Muna kira ga gwamnatin jam'iyar APC na jihar Kebbi, idan dai tana da bukata da kuri'armu, ta kiramu ta zauna da mu ta biya mu kudaden mu, idan bata bukata da mu dole mu yi hakuri. Idan ba a kira mu aka gaya mana matsayi kudaden mu ba, za mu yi kwamiti mai karfi wanda za mu zagaya da mota goma ko ashirin a kowace karamar hukuma a jihar Kebbi mu wayar da kan jama'ar mu cewa ga ajam'iyar da za mu yi . Ina kira ga magoya bayana cewa kowa ya iya bakinsa, muna cikin jam'iyar APC. Ni dai a matsayina na shugaba, har yanzu ina APC amma idan babu wani bayani takamamme dangane da wannan bashi, gaskiya ba za mu yi APC ba a zabuka da ke tafe".
Wadannan bayanai na shugaban kungiyar, sun sami karbuwa domin jama'a sun dinga amsa cewa "Gaskiyane ko haka ne" a duk lokaci da ya saka aya a bayaninsa.
A nata jawabi, shugaban Mata na kungiyar masu Fidin na 2015 Hajiya Maryan Umar, ta roki gwamnati ne cewa ta biya su kudadensu. " Muna kira ga gwamnatin jihar Kebbi cewa ta biya 'yan kwangilar fidin kudadensu domin talakawanta ne, biyan kudin zai sa su huta da matsalar rayuwa. Nan da kwana biyar idan har ba'a dauki mataki ba za mu dauki matakin ficewa daga jam'iyar APC gaba dayan mu da mu da iyalanmu insha Allahu".
Yunkurin mu na jin ta bakin Sakataren Gwamnati jihar Kebbi kan zancen ya ci tura domin mun kasa samun layinsa na salula saboda rashin kyaun layin sadarwa.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi