Rundunar 'yansandan jihar Ebonyi ta damke wasu mutum biyu bayan an kamasu suna dasa bamabamai a karkashin wata gada a garin Idembia a karamar hukumar Ezza ta yamma ranar Juma'a.
Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ya shaida haka a yayin da yake yi wa jama'ar jihar jawabi a kan matsayin tsaro a jihar ta kafofin watsa labarai.
Gwamnan ya ce nassarar kama wadannan mutane ya biyo bayan wani rahoton sirri ne da suka samu cewa 'yan wata jam'iya na shirin dasa ababen fashewa kamar bamabamai a wasu zababbun wurare a fadin jihar.
Yanzu haka yansanda na gudanar da bincike bayan cafke wadaannan mutane biyu.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi