• Labaran yau

  Zargi: Magidanci Ya Yi Wa Matar Makwabcinsa Duka Har Ta Suma A Jihar Kaduna

  'Yansanda a jihar Kaduna sun gurfanar da wani magidanci 'dan shekara 35 mai suna Gabtiel Elijah a gaban wata Kotun gargajiya ranar Alhamis, bayan an zarge shi da yi wa matar makwabcinsa duka har ta suma a unguwar Barnawa.

  'Dansanda mai gabatar da kara Sajent Chidi Leo, ya shaida wa Kotu cewa lamarin ya faru ne ranar 27 ga watan Disamba 2018, a gidansa da ke rukunin gidajen Barnawa, yana fuskantar tuhumar cin zarafi ta hanyar duka.

  Matar da ta sha duka a hannun makwabcinta mai suna Amaka Chinoso, ta kai kara ne a wajen 'yansanda bayan ta yi zargin cewa Elijah ya yi mata duka har ta suma. Ta yi zargin cewa sun sami matsala ne ta cacar baki tare da Elijah, wanda shi kuma ya harzuka ya dinga dukanta har ta suma.

  Alkalin Kotun Mr Ibrahim Emmanuel, ya bayar da belin Gabriel Elijah a kan Naira 100.000 tare da shaidar biyan haraji ga Gwamnatin jihar Kaduna

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Zargi: Magidanci Ya Yi Wa Matar Makwabcinsa Duka Har Ta Suma A Jihar Kaduna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });