• Labaran yau

  'Yunwa Da Talauci Ne Ya Sa Na Saci Kwalbar Mangyada Na Boye A Tsakanin Kafafuna - Wata Barauniya

  Sashen jakar magori na isyaku.com ya leka birnin Lagos inda ya samo mana labarin wata mata da ta wulakanta kanta bayan ta saci kwalbar man gyada ta boye a tsakanin kafafunta a wani kasuwar zamani watau super market ranar Litinin.

  Wata ma'aikaciyar wannan kasuwar ce ta kula cewa matar ta kasa yin tafiya kamar yadda ya kamata, kuma ba haka take tafiya ba a lokacin da ta shigo kasuwar. Sakamakon haka ma'aikaciyar ta fuskanci wannan mata, domin tana zargin cewa da walaki, wai goro a cikin miya.

  Bayan an tsananta tambayoyi da bincike ne fa sai aka caje wannan mata, kash abin kunya! sai ga kwalbar man gyada ta boye a tsakanin kafafunta da al'aurarta kamar yadda kake gani a wannan hoto.

  Amma fa wannan matar, roko ta yi cewa a yafeta, ta ce "Yunwa da talauci ne ya sa na saci wannan kwalbar mangyada, na san abin da na aikata ba daidai bane, ina rokonku ku yafe mini, kun fi karfin wannan kwalbar mangyada, don Allah ku rufa mini asiri ku yafe ni. Wallahi ina da 'yaya uku, kuma mahaifinsu ya rasu.Don Allah ku yafe mini kada ku kai ni wajen 'yansanda domin za su kai ni Kurkuku, sakamakon haka makomar yarana zai tabarbare. Wallahi ban taba yin sata ba, yau ne na ce bari in jarraba daukar wannan kwalbar mangyada".

  Wa'dannan su ne kalamai masu ban tausayi da suka fito daga bakin wannan mata.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: 'Yunwa Da Talauci Ne Ya Sa Na Saci Kwalbar Mangyada Na Boye A Tsakanin Kafafuna - Wata Barauniya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });