• Labaran yau

  Yarda Da Tsibbu Ya Sa Mahaifi Ya Kashe 'Ya'yansa 2 Bisa Zargin Cewa Yaran Mayu Ne

  'Yansanda a jihar Bayelsa, sun kama wani magidanci mai suna Sunday Otasi 'dan shekara 42, bayan ya kashe 'ya'yansa guda biyu da guban 'Sniper" bisa zargin cewa 'ya'yanshi Mayu ne.

  'Dansa na uku ya tsira bayan ya tsere daga cikin daji da mahaifinsa ya daaure shi tare da kannensa amma yana Asibiti rai a hannun Allah.

  Otasi 'dan asalin garin Agbobiri-Okodia ne a karamar hukumar Yenagoa a jihar Bayelsa, ya kai yarasa su uku cikin daji inda tare da taimakon kaninsa watau Kawun yaran, ya dauresu a jikin itaciya a daji da ke kan hanyar Glory Drive Igbogene, a Yanagoa. Yaran su ne Success shekara 'dan 14, Miracle 'dan shekara 12 da Godsome mai shekara 10.

  Bayanai sun ce bayan mahaifin yaran Otasi ya daure su tareda taimakon kaninsa watau Kawun yaran mai suna Levai Ayah, sai mahaifin yaran ya tilasta su cewa su sha wani abu da ake kyautata zaton guban Sniper ne a cikin wani kwalba.

  Majiyar isyaku.com ta ce wa'dannan yara sun fara samun matsala ne a bara bayan mahaifinsu ya je wajen wani malamin Addinin Kirista mai suna George Odoko na Chochin George Odoko Outreach Ministries , shi kuma ya shaida masa cewa  'yayansa Mayu ne kuma su ne suka saka masa rashin lafiya da yake fama da shi.

  Tun wannan lokaci ne wa'dannan yara suka fuskanci gallazawa, duka, tozarci da wulakanci daga wajen mahaifinsu Otasi tare da 'yan uwanshi mahaifinsu gaba daya, wa'danda suka yi amanna cewa mahaifiyarsu ce ta saka masu maita kafin ta rabu da mahaifinsu Otsai domin sun dade da rabuwa.

  Yanzu dai 'yansanda na bincike a kan wannan lamari na yarda da tsibbu wacce ta kai mahaifi ya kashe 'ya'yan da Allah ya bashi a Duniya.  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yarda Da Tsibbu Ya Sa Mahaifi Ya Kashe 'Ya'yansa 2 Bisa Zargin Cewa Yaran Mayu Ne Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });