'Yan Iska Sun Watse Taron Kaddamar Da Kampen Na APC A Jihar Lagos

Harbe harbe da bindigogi sakamakon tashin hankali da ya auku a taron kaddamar da kampen na jam'iyar APC na jihar Lagos ya sa ala tilas taro ya watse. Taron an fara shi ne a filin SkyPower da ke GRA a Ikeja na birnin Lagos ranar Talata.

Daily Trust ta ruwaito cewa jami'an tsaro sun yi yi ta harbi a sama domin su raba wata rigima da ta barke kuma ta rikide zuwa tashin hankali tsakanin matasan wasu bangarori da basu ga maciji da juna a kungiyar NURTW, wa'danda ke wajen taro. Sakamakon hargitsi da tashin hankalin ya haifar ne ya sa jami'an 'yansanda da na Civil Defence suka fara harbi a sama.

Wannan ya sa taro ya watse domin jama'a sun ranta na kare yayin da 'yansanda suka dinga kama na kamawa suna saka su a cikin motarsu, wasu kuma suka dinga ketare katangar filin suna fadawa a bangaren titin Oba Akinjobi.

Bayanai sun ce ana fargaban cewa an kai ma wani jigo a kungiyar NURTW na jihar Lagos Musiliu Akinsanya da aka fi sani da suna Oluomo hari, amma kokari manema labarai na jin ta bakinsa ya ci tura.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN