• Labaran yau

  Yadda ziyarar shugaba Buhari jihar Kebbi ta kasance. Hotuna da bidiyo

  Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Kebbi ranar Laraba inda ya kaddamar da yakin neman zabe na shugaban kasa tare da Gwamna Atiku Bagudu 2019. Buhari ya isa babban filin wasa na Haliru Abdu da ke garin Birnin kebbi sanye da farar babban riga da hula rike da Tsintsiya alamar jam'iyar APC bayan La'asar tare da tawagarsa.

  Shugaba Buhari ya gode wa jama'ar jihar Kebbi bisaa kyakkyawar tarbo da aka yi masa, ya kuma gode wa manoman jihar Kebbi bisa dagewa da suka yi kan harkan noman shinkafa " Sakamakon noman shinkafa da Manoma ke yi a jihar Kebbi, an daina shigowa da shinkafa wanda hakan ya jawo ma Najeriya martaba ta dogaro da kai kan harkan shinkafa".


  'Za mu gina layin dogo daga Zamfara zuwa jihar Kebbi" a cewar shugaba Buhari.

  Shugaban jam'iyar APC Adams Oshiomhole wanda ya dinga tsalle yana sheka rawa kafin ya fara jawabi a wajen taron ya ce " Marasa gaskiya na tsoron shugaba Buhari ne domin baya sata kuma baya barin a yi sata, sakamakon haka duk wani barawon dukiyar talakawa bai da mafaka a karkashin mulkin Buhari".


  Ministan sufuri Rotimi Amaechi, shugaban jam'iyar APC Adams Oshiomhole, tsohon Gwamnan jihar Borno Ali Modu Sheriff, Ministan cikin Gida da Ministan tsaro na cikin manyan baki da suka halarci gangamin yakin neman zaben na yau. Hakazalika manyan ma'aikatan Gwamnatin jihar Kebbi da 'yan siya na jihar Kebbi suna cikin wannan taron.  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda ziyarar shugaba Buhari jihar Kebbi ta kasance. Hotuna da bidiyo Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });