• Labaran yau

  Yadda Dan Takaran Kujerar Gwamna a Jam'iyar APC Ya Kure Mutuwa A Hannun Matasa A Taraba

  Legit Hausa
   
  Jakadan Najeriya zuwa kasar Trinidad and Tobago, Hassan Ardo, da dan takaran gwamnan jihar Taraba karkashin jam'iyyar APC, Sani Danladi, ya tsallake rijiya da baya a ranan Alhamis, 17 ga watan Junairu yayinda matasan karamar hukumar Wukari suka kai musu mumunan hari.

  Mun samu rahoton cewa wasu mafusatan masata wadanda ake zargin yan jam'iyyar People’s Democratic Party, PDP, sun far wa motar dan takaran yayinda suka nufi karamar hukumar Ibi na jihar Taraba. Wani idon shaida da ya laburtawa jaridar Daily Nigerian cewa abin ya faru ne lokacin da dan takaran wanda yake yakin neman zabe a kudancin jihar ya kutsa cikin matasan yayinda suka tare shataletatalen da ke karamar hukumar Ibi.

  Tabbatar da hakan, shugaban matasan jam'iyyar APC, Habu Pari, wanda ya samu raunuka a kansa ya bayyana cewa matasan na rike da muggan makami kuma suka budewa motarsu wuta. Game da cewarsa, matasan sun raunata mutane da dama kuma suka bankawa motoci 10 wuta kuma suka sace dukiyoyin mutanen da ke cikin motan.

  Yace: "Da farko an cecemu a ofishin hukumar DSS dake nan Wukari, amma duk da hakan, a gaban ofishin suka kona motocinmu." Sun tare hanyoyi kuma kuma kai mana hari. A yanzu haka da yamman nan, akalla mutane 15 sun jikkata sakamakon harbin bindiga.  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda Dan Takaran Kujerar Gwamna a Jam'iyar APC Ya Kure Mutuwa A Hannun Matasa A Taraba Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });