• Labaran yau

  Yadda Aka Yi Ma Saurayi Zindir A Gari Bayan An Kama shi Yana Tsintar Bahaya. Hotuna

  Da tsakar ranar yau a unguwar Matthew da ke Ado Ekiti babban birnin jihar Ekiti wasu fusatattun matasa suka wulakanta wani bawan Allah matashi, bayan an gan shi yana tsintar busashshen bahaya na bil'adama yana sakawa a cikin bakar laida.

  Wadannan samari sun yi masa mumunar duka, suka tube shi zindir suka zagaya da shi a cikin unguwar ta Matthew, yayin da 'yan mata suka yi ta daukar bidiyo da hotunan wannan bawan Allah.

  Isyaku.com ya gano cewa an yi masa wannan wulakanci ne bisa zargin kasancewa 'dan kungiyar asiri.

  Amma wata majiya ta shaida wa isyaku.com cewa, wasu manoma sukan yi amfani da busashshen bahaya na bi'adama a zaman taki a gonakinsu. Kuma garin nemo wannan bahaya dole sai an shiga bola-bola na unguwanni kafin a iya tattarawa, kuma garin neman bahaya, wasu sukan fada hannun mutane da ke masu mumunar fahimta da kan kai ga zargi kamar yadda aka yi ma wannan 'dan talikin a unguwar Matthew.

  DAGA ISYAKU.COM

   Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Yadda Aka Yi Ma Saurayi Zindir A Gari Bayan An Kama shi Yana Tsintar Bahaya. Hotuna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });