Hausa Legit
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shugabannin hukumar
kula da ci gaban yankin arewa maso gabashin kasa da rikicin Boko Haram ya
daidaita. Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki nae ya bayyana haka yayin
karanta wasikar da shugaban kasar ya rubuta wa Majalisar domin tantance
sunayen.
Sunayen wadanda
Buhari ya gabatar sune Manjo Janar Paul Terfa a matsayin shugaba, sai kuma
Mohammed Goni Alkali a matsayin Babban Daraktan Gudanarwa tare da Musa Uma
Yashi a matsayin Daraktar Jinkai da Mohammed Jawa a matsayin Daraktan kudi da
mulki.
Sauran sun hada hada da Umar Maiwada Mohammed a matsayin
Daraktan Ayyuka da kuma wakilan shiyoyi 6 na yankunan kasar, wato David Sabo
Kante daga Arewa Maso Gabas da Asamo Mohammed daga Arewa Maso Yamma da Benjamin
Adeniyi daga Arewa ta Tsakiya da Olawale Osun daga Kudu Maso Yamma, sai Theo
Nkechi daga Kudu Maso Gabas da Bassey Uke daga Kudu Maso Kudu.
Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya ya tagayyara sakamon
dogon lokacin da mayakan Boko Haram suka dauka na kaddamar da hare-hare, abin
da ya haddasa asarar rayukan dimbin jama'a tare da gurgunta tattalin arzikin
yankin, baya ga tilasta wa miliyoyin mutane kaurace wa gidajensu.