• Labaran yau

  Rana Ta Bace, 'Yansanda Sun Kashe Wani Kusurgumin 'Dan Fashi Da Ake Nema

  Wannan ba ainihin hoton 'Dan mai keke bane
  'Yansandan jihar Katssina sun bindige wani kusurgumin 'dan fashi mai suna Kane Muhammed mai shekara 35, da aka fi sani da suna 'Dan mai keke wanda sunansa ke cikin jerin sunayen 'yan fashi da 'yansanda ke nema ruwa jallo a jihar Katsina.

  Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Katsina Supritendant Gambo Isah ne ya shaida wa manema labarai haka a birnin Katsina.

  Ya ce "Lamarin ya faru ne ranar 4 ga watan Janairu a unguwar tsohuwar Kasuwa, inda wata maboyar masu aikata miyagun laifi take a garin Bakori, a karamar hukumar Bakori. Yayin da 'yansanda ke gudanar da sintirin zagaye, sai suka ci karo da gungun da 'Dan mai keke ke jagoranta, wanda suka far ma 'yansanda da miyagun makamai, lamari da ya sa 'yansanda suka harbi 'Dan mai keke, amma ya mutu yayin da yake jinya a wani Asibiti a garin Bakori".

  Yanzu haka yansanda sun dukufa wajen neman sauran 'yan gungun da suka tsere.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Rana Ta Bace, 'Yansanda Sun Kashe Wani Kusurgumin 'Dan Fashi Da Ake Nema Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });