• Labaran yau

  Mutane Da Dama Sun Mutu Wajen Dibar Man Fetur A Tilera Da Ta Fadi Daga Bisani Ta Yi Bindiga

  Wata motar tanka dauke da man fetur ta yi bindiga kuma ta kama da wuta yau a kan hanyar  Calabar zuwa Odukpani a karamar hukumar Odukpani na jihar Cross Rivers, lamari da ya haifar da mutuwar mutane da dama.

  Isyaku.com ya gano cewa jama'ar kauye da ke kusa da inda tankar ta fadi suka yi riga-riga wajen diban man fetur da ya malale a kasa, kuma wasu suna amfani da kwano da bokiti wajen diban man, daga bisani sai wuta ta tashi ta rufe wasu masu diban man kuma ta kone su kurmus.

  'Yansanda sun yi kokari wajen shawo kan lamarin  musamman bayan wuta ta lakume mutane da dama. Wadanda suka tsira da kunar wuta suna Asibitin koyarwa na jami'ar Calabar.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mutane Da Dama Sun Mutu Wajen Dibar Man Fetur A Tilera Da Ta Fadi Daga Bisani Ta Yi Bindiga Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });