• Labaran yau

  Matar Aure Ta Bankawa Mijinta Wuta Ya Mutu Domin Ya Ki Ya Gaya Mata Password Na Wayarsa

  Wata matar aure mai suna Ilham Cahyani mai shekara 26 ta watsa wa mijinta Dedi Purnama mai shekara 26 petur daga bisani ta banka masa wuta ta hanyar kunna kyastu ta jefa masa sakamakon haka wuta ta kama jikinsa haikan domin mijinta ya ki ya gaya mata lambobin da ya rufe wayarsa da su.

  Mijinta Dedi Purnama ya mutu a wani Asibiti bayan kwana biyu yana jinya a gabacin Lombok a yankin Yammacin gundumar Nusa Tenggra na kasar Indonesia.

  Shugaban 'yansandan yankin gabacin Lambok Chief Made Yogi ya ce " Rigimar ta taso ne bayan maigidan matar yana kan rufin dakinsu yana gyara, sai ta tambaye shi lambar sirri da ya rufe wayarsa ta salula da ya bari a cikin daki, shi kuma sai ya ki gaya mata lambobin sirri da ya rufe wayarsa watau Password".

  "Daga nan ne kalamai masu zafi suka fara fitowa daga bakinta babu kakkautawa, shi kuma mai gida ya cika da haushin zargi da cin mutunci da matarsa ta ke ta yi masa, daga bisani sai ya sauko ya nufi wajenta ya kwada mata mari. Ita kuma ta fita a guje ta dauko galan na petur da suke amfani da shi domin zuba ma Tahunar gidansu mai, sai ta watsa ma mijinta kuma ta kunna masa wuta da kestu ta jefa masa a jikinsa. Nan take wuta ya rufe mijinta, kafin jama'a su rugo su taimaka wajen kashe wuta da ta riga ta ci jikinsa".

   
  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Matar Aure Ta Bankawa Mijinta Wuta Ya Mutu Domin Ya Ki Ya Gaya Mata Password Na Wayarsa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });