• Labaran yau

  Kalli Dino Melaye Kwance A Kasa Bayan Jami'an Tsaro Sun Dauke Shi Daga Asibitin 'Yansanda

  Rahotanni daga birnin Abuja sun ce jami'an 'yansanda sanye da abin rufe fuska sun dauke Sanata Dino Melaye daga Asibitin da yake jinya da ranar yau, suka saka shi a cikin wata mota da bata dauke da kowane alama suka tafi da shi kamar yadda wani ganau ya ce.

  An gan hutunan Dino Melaye kwance a kasa, a cikin harabar Asibitin hukumar tsaro ta DSS da ke Abuja.

  Kakakin hukumar 'yansanda Mr. Jimoh Moshood ya shaida wa gidan Talabijin na Channels cewa an dauke Sanatan daga Asibitin 'yansanda ranar Juma'a.

  Jimoh ya ce hakan ya biyo bayan jayayya ne da aka samu tsakanin 'yansanda da Dino Melaye, domin 'yansanda sun ce Sanatan ya ji sauki kuma zasu gurfanara da shi a gaban Kotu, amma Sanatan ya ce yana bukatar karin lokaci domin ya yi jinya. Sakamakon haka ne aka kai shi wani Asibitin Gwamnati.

  Wata babban Kotun Tarayya a Abuja, ta ba 'yansanda waranti domin su kama kuma su tsare Sanata Dino Melaye har tsawon kwanan 14 daga ranar da suka kamashi..

  'Yansanda na zargin Sanatan da hannu a wani hari da aka raunata wani jami'in 'dansanda a Lokoja watanni da suka gabata bayan an harbi dansandan da bindiga.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kalli Dino Melaye Kwance A Kasa Bayan Jami'an Tsaro Sun Dauke Shi Daga Asibitin 'Yansanda Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });