Jihar Kebbi 2019: 'Dan Bagudu Ya Bukaci A Zabi APC Sak A Karamar Hukumar Kalgo

Jam'iyar APC mai mulki a jihar Kebbi a ci gaba da yakin neman zabe da take yi a cikin fadin jihar, ta gudanar da gangamin yakin neman zabe a karamar hukumar mulki ta Kalgo karkashin jagorancin Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi.

Gwamna Bagudu sanye da babbar riga mai ruwan toka da ta sha aikin kwado da linzami mai farar kala kuma sanye da farar hula rike da Tsintsiya alamar jam'iyar APC, ya zagaya zuwa cikin babban filin wasa na makarantar sakandare da ke garin Kalgo da safiyar yau, inda ake gudanar da taron yakin neman zaben na jam'iyar APC.

Gwamna Bagudu ya bukaci jama'a su zabi jam'iyar APC sak, daga shugaban kasa har Gwamna, Sanatoci, yan Majalisar Wakilai, da yan Majalisar Dokoki  na jiha.

Taron ya sami halartar manyan 'yan siyasa na jihar Kebbi, manyan jami'an gwamnatin jihar Kebbi, kwammishinoni, da sauran 'dimbin jama'a da suka sami halartar gangamin yakin neman zaben.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post