Legit Hausa
Bayan taron majalisar zartarwa (FEC) da shugaba Buhari ya
jagoranta a jiya, Talata, gwamnatin tarayya ta sanar da niyyarta na mika
shawarar da ta yanke a kan karin albashi ga kwamitin masu ruwa da tsaki a
harkar tattalin arziki(NEC).
Jaridar Punch ta rawaito cewar a wurin taron FEC na jiya,
gwamnatin tarayya ta amince zata biya N30,000 a matsayin mafi karancin albashi
kuma zata sanar da NEC a ganawar da zasu yi gobe, Alhamis, 17 ga watan Janairu.
NEC ta kunshi gwamnonin jihohin Najeriya, gwamnan babban
bankin kasa (CBN), wasu manyan ministoci, da ma'aikatu da hukumomin gwamnati.
Da yake magana da manema labarai a kan batun, ministan yada yada labarai da
al'adu, Lai Mohammed, ya ce za a tattauna batutuwa da dama da FEC ta amince
dasu.
A cewar sa, "ba zan iya baku cikakkun bayanai a kan
abubuwan da muka tattauna ba tunda zamu tattauna a kansu a ganawar mu da NEC ta
ranar Alhamis. Zamu sanar da shawarwarin da muka yanke bayan ganawar."Ko a
ranar 13 ga watan Disamba na shekarar 2018, sai da gwamnonin Najeriya suka yi
wani taro a Abuja domin cigaba da tattaunawa a kan batun na karin albashi.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi