Fasakwabrin Tilera 8 Cike Da Shinkafa, Kwastam Sun Bindige Mutum 5 Har Lahira. Hotuna


Jami'an rundunar hana fasakwabri na a jihar Ogun sun bindige wasu mutum biyar har lahira wa'danda ake zargin sun yi satar shigowa da manyan motocin Tilera guda takwas makare da shinkafa a garin Owode Idiroko.

Rahotanni sun ce sashen sintiri da kuma sa ido kan harkar fasakwabri na rundunar Kwastam sun kai harin bincike a wani kebantaccen gida ranar Lahadi da karfe 2:30 na Asuba a Asero da ke cikin birnin Abeokuta kuma suka sami motocin Telera guda takwas makare da shinkafa da aka yi satar shigowa da su.

Kakakin rundunar Kwastam na jihar Ogun Abdullahi Aliyu Maiwada ya ce " Yayin da jami'an mu suka yi kokarin kama kayakin shinkafar sai wasu mutane suka afka masu ".

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post