• Labaran yau

  Daga Karshe, Dino Melaye Ya Yanke Jiki Ya Fadi Bayan Yansanda Sun Kamashi.Hotuna+Bidiyo

  Jan daga da 'yansanda suka yi a kofar gidan Sanata Dino Melaye a mashigar Sangha da ke unguwar Maitama a birnin Abuja ya zo karshe a yau Juma'a 4 ga watan Janairy 2019, bayan Sanata Dino Melaye ya bude kofar gidansa ya fito da kanshi a gaban wasu Sanatoci na jam'iyar PDP, jami'an 'yansanda da 'yan Jarida.

  Sanata Dino Melaye ya yanke jiki ya fadi a lokacin da ya fito daga gidansa, amma jami'an 'yansanda sashen SARS sun taimake shi suka rike shi saannu a hankali aka saka shi a cikin mota suka tafi da shi ofishin 'yaansanda sashen SARS da ke Guzape a Abuja.

  Dino Melaye na fuskantar tuhuma daga 'yansanda bayan an zarge shi da hannu a harbi da bindiga da wasu 'yan daban siyasa suka yi ma wani jami'in 'dansanda MOPOL a jihar Kogi 'yan watanni da suka gabata kuma harbin ya raunata shi.

  Sanata Dino dai ya dade yana takun saka tsakaninsa da Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, lamari da ya kai ga kama Sanatan a watannin baya, amma wata babban Kotun tarayya ta bayar da belinsa.

  Hakazalika, 'yansanda sun taba cewa Sanatan ya yi tsalle daga motarsu bayan sun kama shi a Area 1 da ke Abuja a kan hanyarsu ta zuwa birnin Lokoja na jihar Kogi bisa wasu jerin tuhume tuhume da 'yansanda ke yi masa a watannin baya.

  Daga baya bayannan, Sanata Dino Melaye yana daya daga cikin wasu Sanatoci da suka dinga yi ma shugaba Buhari ihu a zaure Majalisa lokacin da Buhari yake jawabi. An ga faifen bidiyo a intanet da ya nuna yadda Sanata Dino Melaye ya dinga yin tsalle yana cewa "Makaryaci" watau "Lair" lokacin da shugaba Buhari ke jawabi a zaure Majalisa.
   


  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Daga Karshe, Dino Melaye Ya Yanke Jiki Ya Fadi Bayan Yansanda Sun Kamashi.Hotuna+Bidiyo Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });