• Labaran yau

  Batagari Sun Kashe Wata Mata Uwar Yara 4 Bayan Sun Yi Mata Fyade

  Wasu 'batagar sun halaka wata mata uwar yara hudu mai suna Glory Omo-Ohwu a birnin Yenagoa na jihar Bayelsa. Rahotani sun ce matar 'yar asalin  garin Oreba/Uhweru ce na jihar Delta.

  Wannan matar wacce ke zaune a Akenfa-I Epie da ke jihar Bayelsa tana da aure kuma uwar yara hudu ce wacce ke sana'ar sayar da kifi. Rahotanni sun ce matar ta tashi da misalin karfe 5 na Asuba domin ta gasa kifi da take kaiwa kasuwar Mbiama domin sayarwa ranar Talata 29 ga watan Janairu.

  Amma sai bata dawo gida ba har rana ta fito. Bayan yaranta sun kula mahaifiyarsu bata dawo ba, kuma dama maigidanta ya yi tafiya.

  Daga bisani ne aka gano gawarta a wani kangon gida da ba a kammala ba da ke kusa da gidanta a wani mumunar yanayi da ake zargin cewa wasu mugayen batagari sun yi mata fyade kafin suka yi mata mumunar kisan gilla na rashin imani.

  An shaida ma jami'an tsaro aukuwan lamarin, kuma sun je suka fara bincike.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Batagari Sun Kashe Wata Mata Uwar Yara 4 Bayan Sun Yi Mata Fyade Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });