An Sake Dauke Dino Melaye Zuwa Ofishin 'Yansanda SARS Da Ke Guzape

'Yansanda sun sake dauke Sanata Dino Melaye daga Asibitin SSS da ke Abuja zuwa ofishin SARS da ke Guzape a babban birnin tarayya Abuja.

Asibitn 'yansanda ta ce Dino Melaye ya murmure kuma zai iya fuskantar shari'a. Amma Sanatan ya musanta haka yana mai cewa yana bukatar karin lokaci domin ya kara samun sauki.

Wata babban Kotu ta ba 'yansanda Warantin kama kuma su tsare Sanata Dino Melaye har tsawon kwanan 14.

Sanatan yana fuskantar zargin kasancewa da hannu a wani harin bindiga da aka kai kan wani jami'in 'dansandan Mopol sakamakon haka aka raunata shi a garin Lokoja 'yan watanni da suka gabata, amma Sanatan ya sha musanta wannan zargi.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN