An Nada Frank Mba A Matsayin Sabon Kakakin Hukumar 'Yansandan Najeriya

Mukaddashin Safeto janar na 'yansandan Najeriya Abubakar Adamu Mohammed, ya nada sabon kakakin hukumar 'yansanda na Najeriya ACP Frank Mba ranar Laraba.

Farnk Mba ya karbi mukamin ne daga DCP Moshood Jimoh.

Frank 'dansanda ne da ya yi karatun Lauya a jami'ar Lagos, ya kuma yi Digiri na biyu a Jami'ar Dundee da ke Scotlan a kasar Britaniya, kuma ya yi karatun horon aikin 'dansanda a Makarantar horar da hafsoshin 'yansanda da ke Wudil a jihar Kano.Haka zalika Frank ya sami horo daga Makarantar koyar da dabarun bincike na FBI da ke Quantico a kasar Amurka, ya kuma sami horo daga Jami'ar Harvard kan dabarun tsaro na kasa da kasashen Duniya.

DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post