An Cafke Wani Matashi Da Ya Yi Shigar Mata Bisa Zargin Kasancewa Dan Boko Haram A Maradi

Jami'an tsaro sun cafke wani mutum da ya yi shigar mata wai shi mahaukaci ne yana bin bola bola a cikin birnin Maradi na jamhuriyar Nijar. Dubun wannan mutum ta cika ne bayan wasu jama'a sun kiyaye cewa ya sami wani wuri ya labe yana magana da wayar salula. Sakamakon haka suka kira jami'an tsaro.

Bayan jami'an tsaro sun caje jikinsa, sai suka fidda kayaki daban daban daga jikinsa har da rigar nono, daga bisani ya bayyana cewa ashe na miji ne ya yi wannan shiga irin na mata.

Tuni jami'an tsaro suka yi awon gaba da shi domin fadada bincike duba da cewa jama'ar gari sun yi zargin cewa dan kungiyar boko haram ne.

Kalli bidiyo yadda jami'an tsaro suka kamashi:



DAGA ISYAKU.COM

Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN