• Labaran yau

  Al'umman Garin Kanya Zasu Biya Gwamna Bagudu Bashin Kuri'unsu A Jihar Kebbi - Zainab Kansila


  isyaku.com 21-01-2019


  Kansilar Kanya ward a garin Kanya na karamar hukumar Danko/Wasugu Hajiya Zainab Jibo,ta kaddamar da shirin shiga gida gida domin fadakar da magidanta tare da jama'r gida muhimmancin sake zaben shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa, kuma a zabi Sanata Atiku Bagudu a matsayin Gwamnan jihar Kebbi karo na biyu. Shirin ya fara aiki a garin Kanya da ke karamar hukumar Danko/Wasagu ranar Lahadi 20 ga watan Janairu 2019.

  Hajiya Zainab tare Alhaji Aliyu Jajirma 'dan "babban gida" da taimakon kungiyoyin mata da mataimakin shugaban jam'iyar APC a ward na Kanya, kungiyoyin matasa, Zawarawa, kungiyoyin Kiristoci da karin wasu kungiyoyi na ci gaban kasar Kanya duk sun halarci wannan taro na fadakarwa.


  Kansila ta yi jawabi a kan muhimmancin mallakar katin zabe, ta kara haske musamman ga mata cewa su yi hakuri kada su sa lalle kafin ranar zabe. Kansila ta ce an sami bayani cewa idan mace ta sa lalle kuma ta je wajen kada kuri'a,an gano cewa lalle yakan bata kuri'a da aka dagala.

  Hakazalika, ta bukaci mata su gaggauta zuwa domin su karbi katinsu na zabe, duba da cewa saura 'yan kwanaki kalilan a rufe bayar da katin zaben na dindindim watau PVC.

  Hajiya Zainab ta ce " Idan baki da katin zabe ba yadda za ki zabi shugaba Buhari ko Gwamna Atiku Bagudu, saboda haka ki hanzarta ki je ki karbi katinki na zabe da kika yi rijista kafin a rufe karban katin nan da 'yan kwanaki.


  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Al'umman Garin Kanya Zasu Biya Gwamna Bagudu Bashin Kuri'unsu A Jihar Kebbi - Zainab Kansila Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });