• Labaran yau

  Alfa Ya Cinye N700.000 Bayan Ya Sa Wata Mata Ta Tube Zindir Da Sunan Addu'ar Samun Sa'a

  Wata mata mai suna Aisha Odofin ta kai karar wani Malami mai suna Alfa Adeyemi Mutairu a wajen 'yansanda bayan ya damfareta kudi har N700.000 da sunan zai yi mata addu'a da zai sa ta sami nassara da waraka a rayuwarta. Wannan lamari ya faru ne a unguwar Ejigbo da ke birnin Lagos.

  Majiyar isyaku.com ta ce kafin Malamin ya yi mata  addu'a, ya sa ta tube zindir sai ya yi mata wanka daga bisani ya yi mata addu'a da yake son ya yi. 

  Tun farko dai Malam Adeyemi ya shaida wa Aisha cewa tana dauke da da la'ana ne da ya sa bata samun nassara a rayuwarta, amma bayan ya cika ta da kalamai na tsibbu da saddabaru, daga karshe dai Aisha ta amince da haka kuma ta bayar da hadin kai, har ta kawo masa zunzurutun kudi har N700.000 daga cikin adadin kudi da ya bukata.

  Bayan Alfa Adeyemi ya yi addu'a, amma lamurra fa suka kara jagulewa ga Aisha, daga bisani dai Aisha ta tunkari Alfa Adeyemi cewa ita fa bukatarta bata biya ba, sai ta bukaci mafita kan lamarin inda ta ce Alfa ya maido mata kudinta zunzurutun kudi har N700.000, amma Alfa ya ce fau fau hakan ba za ta yiwu ba domin da kudin ne aka sayi kayakin da aka hada aka yi mata addu'a.

  Bayan Aisha ta yi iya abin da zata iya yi domin Alfa ya maido mata da kudinta amma ya ki, sai Aisha ta garzaya caji ofis na 'yansanda da ke unguwar Ejigbo ta yi karar Alfa. Bayan 'yansanda sun kama Alfa Adeyemi suka gudanar da bincike, sai suka gurfanar da shi a gaban wata Kotun Majestare bisa tuhumar damfara da cin amana.

  Bayan an karanta ma Alfa Adeyemi tuhumar da ake yi masa a gaban Alkali, Alfa bai amsa laifinsa ba, sakamakon haka Alkalin Kotu Mr. L.K.J  Layeni ya bayar da belin Alfa Adeyemi a kan kudi N100.000. da kuma karin wasu mutum biyu da za su tsaya masa a sharuddan belin. Amma an tasa keyar Alfa zuwa Kurkuku kafin ya cika sharuddan beli domin Alkalin ya daga shari'ar zuwa ranar 3 ga watan Fabrairu 2019.

  DAGA ISYAKU.COM 

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews 

   Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG 

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Alfa Ya Cinye N700.000 Bayan Ya Sa Wata Mata Ta Tube Zindir Da Sunan Addu'ar Samun Sa'a Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });