• Labaran yau

  Abin Mamaki, Wata Lauya Ta Kashe Mijinta a Birnin Lagos


  Leadershipayau.com

  Ranar Larabar da ta gabata ne mataimakin sufiritandan ‘yan sanda Olusegun Bamidele, ya bayyana wa wata babbar kotu da ke Igbosere cikin jihar Legas cewa, wata lauya, Udeme Otike-Odibi, wadda ake zarginta da laifin kashe mijinta, ta tabbatar da cewa ta aikata wannan laifin. Udeme yar shekara arba’in da takwas ta na fuskantar tuhuma ne akan zargin dabawa mijinta wuka mai suna Symphorosa Otike-Odibi a gidan sa dake rukunonin gidaje na Diamond fake a unguwar Sangotedo, cikin jihar Legas, inda hakan ya janyo mutuwar sa. 

  Har ila yau, ana zargin Udeme bayan ta cakawa mijin wuakar ta kuma ci zarafin gawar. Laifin nata ya sabawa sassa na 165 (b)/a cikin baka data manyan laifuka ta 223 ta jihar Legas ta 2015. A zaman kotun na ranar Larabar data wuce, Bamidele ya gabatarwa da kotun hujjijin zargin da ake yi matar.

  Titilayo Shitta-Bay ya shedawa kotun cewar shine me jagorantar kisan da aka yiwa mijin kuma duk ya nadi bayanan wadda make zargin lokacin da ya gana da ita kuma a yanzu an bata kariya a asibibitin dake Ikeja, bayan an dauko ta daga asibitin Safeway dake Lekki. Ya ce, alokacin ne Udeme ta rubuta nata bayanin. Ya ce, ta sanar da cewar it’s lauya ce. 

  Ya ce, ta bayyana masa ita matar marigayi Symphorosa ce kuma akwai takaddamar data hadata da mijin kuma shi manemin matan banza ne kuma inta taso masa da maganar, bays nuna wata damuwa. Ta ce, a ranar buyu ga Mayun 2018, lokacin ta na shirin tafiya Birtaniya, ta duba takardar shedar auren su amma bata ganata ba ta kuma tambaye shi takardar amma baice mata komai ba, inda hakan ya janyo sukai chachar baki har ta fusata ta shiga dakin girki ta dauko wika da tukunyar yin suya ta kwada masa a kai. 

  Ta ce ya kira mahaifiyar da ya sheda mata lamarin, daga nan ta ci gaba da kwada masa akai tare da yin amfani da wukar data chaka masa a cikin sa. Ta kara da cewar, daga nan kuma ta yanke masa mazakuntar sa ta Santa masa a tafin hannun sa na dama. Bamidele ya kara shedawa kotun cewar, bayan da lamarin ya auku, Udeme ta turawa kawar ta sako a waya mai suna Maureen Offor cewar ta aikata ta’asa babba. 

  Ya ce, a bisa dogon binciken da akayi, an gano cewar, ta kuma tura wani sakon ta hanyar WhatsAp zuwa ga wayar kanwar mijin nata mai suna Charles Akpoguma India ta bukaci ta yi masu addua Allah ya yafe masu sannan ta kuma tura wani sakon a ways ga mahaifiyar ta dake grain Kalaba Calabar cewar ta yi fada da mijin nata. Shitta-Bay ya kuma gabatarwa da koton ta hanyar Bamidele hujjoji da dama daga matar. 

  Hujojin sun hadada tukunyar girkin, wukar wayoyin hannu hudu da kuma fasgon ta na Nijeriya da Birtaniya. Da aka bukaci Shitta-Bay ya gabatar da hujjojin zargin da ake yiwa Udeme lauya mai Kate ta Olusegun Banjoko ya nuna jayayya akan hakan. Banjoko ya bukaci kotun kada ta amince da hujjojin domin an samo su ne lokacin lauyan ta baya kusa kamar yadda doka ta tanadar. Alkalin kotun Akintoye ya dage zaman sauraron karar zuwa ranar 25 ga Fabarairu don yin dubi akan hujjojin.

  DAGA ISYAKU.COM 

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews 

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG 

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Abin Mamaki, Wata Lauya Ta Kashe Mijinta a Birnin Lagos Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });