• Labaran yau

  Zargin matarsa na soyayya da maza 3, 'dansanda ya banka wa kanshi wata ya kone

  Wani karamin jami'in 'dansanda ya kulle kofar dakinsa ya banka ma kansa wuta ta kone shi har ya mutu, bayan ya gan wasikun whatsapp na soyayya daga wasu maza guda uku a wayar salula na matarsa a garin Nyatsime na Chitungwiza a kasar Zimbabwe.

  Jami'in 'dansandan mai suna Tinashe Jala yana aiki ne a ofishin 'yansanda na Chitungwiza sashen harkar yanar gizo ICT, kuma ya yi satar shigar kutse a shafin whatsapp na yanar gizo na matarsa whatsapp web, inda ya gano wasu wasikun soyayya da wasu maza daban daban har guda uku suka rubuto wa matarsa mai suna Sibongile Shana, wacce ma'aikaciyar 'yarsanda ce.

  Bisa wannan dalili ne rigima ya kaure tsakaninsu, lamari da ya sa 'yan uwansu suka shiga tsakani, har wata kanwar shi ta dauki 'ya'yanshi su biyu ta tafi da su gidanta tana mai cewa rigimar iyayensu bai kamata ya shafe su ba.

  Saidai bayan Tinashe ya raka matarshi Sibongile zuwa wajen shiga mota, sai ya dawo gida ya daga bisani ya kulle kofar shiga dakinsa da makulli, ya yi ihu, sai ya banka wa kanshi wuta.

  Bayan wasu mata sun gan bakin hayaki yana fitowa daga gidan , kuma suka yi ta kokarin su kashe wutar , amma sai suka tarar  cewa kofar gidan a kulle yake. Sakamakon haka Tinashe 'dan shekara 30 ya mutu bayan ya kone kurmus.

  DARASI

  Mujallar ISYAKU.COM na shawartar magidanta su jure idan matansu sun ci amanarsu, tabbas babban abin bakin ciki ne ka gano cewa matarka tana soyayya tare da wasu maza ba ma wani na miji ba, har da wasikar soyayya. To amma sa'ilin da hankali ya gushe, sakamakon bakin ciki, abu ne mai tsananin wuya, amma, kashe kanka ba shi ne mafita ba.

  Domin idan ka kashe kanka, ka ba masoyanta dama su mallake ta har abada domin ka aika kanka barahu, kuma ka bar ta da wanda take so, kuma sakamakon haka ya sa ta ci amanarka tun da farko.

  Mafita a nan shine, idan haka ta faru, gwamma ka tona mata asiri ka barta da Duniya, domin bayan asirinta ya tonu, kuma tana da igiyar aurenka ta aikata abin da ta yi, ita ce za ta fuskanci kunci, domin hatta saurayin nata zai ji kunyan sakamakon yadda jama'a za su dinga nuna shi cewa Kwarto ne.

  Daga bisani sai ka kara aure, ita kuma ka gaggauta sakinta, idan ba haka ba, za ta iya kawo maka Shege a gidanka, ba tare da sanin cikin da ta dauka ba naka bane. Allah ya kiyaye mu gaba daya amin.


  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Zargin matarsa na soyayya da maza 3, 'dansanda ya banka wa kanshi wata ya kone Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });