• Labaran yau

  Zargin Fashi Da Makami, Matasa Sun Kashe Budurwa Suka Kone Gawarta

  Fusatattun jama'a sun yi ma wata budurwa dukan ajali, daga bisani suka kone gawarta bisa zargin ta taimaka ma wasu 'yan fashi suka kwace babur a hannun wani matashi a karamar hukumar Obudu da ke jihar Cross Rivers ranar Lahadi.

  Budurwar mai suna Miss Vivian ta kammala karatunta na NCE a FCE Obudu, ana zarginta da hannu wajen kashe wani 'dan acaba a garin Obudu a farkon watan Disamba 2018.

  Vivian wacce aka fi sani da suna China, ta gamu da ajalinta ne bayan an bukaci ta fadi wajenda saurayinta yake, amma sai ta ki, sakamakon haka matasa da suka fusata suka afka mata da duka da ya zama ajalinta, daga bisani kuma suka banka wuta a gawarta.

  Hakazalika, majiyarmu ta ce ana zargin Vivian da hannu wajen kashe wani mutum mai suna Mr Peter Akikieye, wanda aka yi ma kisan gilla yayin da ya nuna turjiya lokacin da saurayin Vivian ke kokarin kwace babur da yake acaba da shi a farkon watan Disamba.

  DAGA ISYAKU.COM

  Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

  Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Zargin Fashi Da Makami, Matasa Sun Kashe Budurwa Suka Kone Gawarta Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });