Yin lalata ko zina a cikin mota a kebabben waje ba laifi bane a Najeriya- Hasfan Dansanda

Sakamakon wani labari da muka wallafa na wasu masoya da aka wulakanta su, bayan an kama su suna zina a cikin motar saurayin da rana tsaka, shugaban sashen koke koke na jama tare da martanin gaggawa na rundunar yansandan Najeriya Mr. Abayaomi Shogunle, ya ce babu laifi domin masoya sun sadu, ko sun yi zina a cikin mota ko a waje da ba a daki ba.

Amma hafsan ya kara bayani, ya ce bisa sharadin cewa:

1. wajen da aka aikata saduwar, ko zina ba a wajen da ake yin Ibada bane

2. Wadanda ke saduwar ko aikata zinan sun kai shekara 18 ko fiye.

3. Matukar dukannin masu aikatawa, saduwa ko zina sun amince su aikata zinan tsakaninsu.

4. Matukar ba jinsi daya bane, na miji da na miji, ko mace da mace, watau ya kasance namiji ne da mace.

Daga karshe hafsan ya ce, duk wanda ke fuskantar barazana domin an kama shi sakamakon aikata saduwa ko zina a cikin mota ko a wani kebabben waje, ya gaggauta aika kokensa ga sashen kula da koke koke na musamman na yansanda a @PoliceNG_PCRRU.

DAGA ISYAKU.COM Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/KIHbQShlAs2GexpIYyxleG

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post